The fifth is currently receiving treatment at the hospital. Below is the post published on Hausa Facebook page:
lmajirai Biyar Ne Aka Yi Wa Kisan Gilla A Jihar Naija Daga Habu Dan Sarki Wani rahoton da sashin Hausa na Muryar Amurka ya fitar dangane da yankan ragon da aka yi wa wadansu almajirai dake karatun allo a jihar Naija ya bayyana cewa wannan al’amari dai ya faru ne a garin Tungar Magajiya, da ke yankin karamar hukumar Rijau. Maharan da suka aikata wannan ‘danyen aikin da ba a san ko su waye ba, sun afkawa almajiran ne a lokacin da suke barci suka yan-yanka musu wuya da wani abu da ake kyautata tsammanin ya yi kama da mashi. Malam Muhammadu Bala, wanda yake ‘daya daga cikin malaman almajiran, ya ce cikin dare ya farka ya ji yaran sun farka suna kuka inda ‘daya daga cikinsu yace “Wayyo an kashe wane”. Kuma ya tabbatar da cewa lamarin ya faru a makarantu biyu, wanda a makarantarsa aka yanka yara biyu, sauran ukun kuwa a wata makaranta ta daban abin ya faru
No comments:
Post a Comment